Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharhin Gwamnatin Amurka: Kawo Zaman Lafiya a Yankin Sahel


Fadar White House
Fadar White House

Amurka na aiki tare da yankin Sahel na Afirka – wani yankin muhalli wanda ya faro daga gabar tekun Atlantika na Senegal da ke yamma, zuwa gabar Bahar Maliya a Sudan. Hakanan galibi ana nufin kasashe biyar na Yammacin Afirka waɗanda suka haɗa da Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania, da Niger ake kira G5-Sahel.

"Mun zo nan ne don muyi aiki tare da ku don taimakawa kawo tsaro, kwanciyar hankali, da kyakkyawan shugabanci ga mutanen yankin na Sahel," in ji mataimakin Sakataren mai kula da harkokin siyasa David Hale a cikin jawabin da ya yi na hadin gwiwar kasashen duniya na Sahel.

Rashin zaman lafiya ya fadada a yankin Sahel, duk da haɗin gwiwar ƙawancen don su dakatar da hanyoyin sadarwa na ‘yan ta'adda. Adadin mutanen da suka rasa mazaunansu a yankin tsakiyar Sahel din ya ninka sau 11 sama da wanda aka samu shekaru biyu da suka gabata. Adadin mutanen da ke fuskantar tsananin yunwa ya ninka sau uku a cikin shekarar da ta gabata.

Cikin wadannan mawuyatan yanayin, mataimakin Sakatare Hale, ya sanar da sama da dala miliyan 80 a karin taimakon jinkai ga yankin. "Yayin da muke aiki don rage wahala, mun sake alkawarin goyon bayan abokanmu na Afirka a aikinsu na wajen magance ba kawai wahala ba, da ma abubbuwan da ke janyo rikice-rikice," in ji shi.

Jama'ar karkara suna buƙatar samun abubbuwa na yau da kullun a cikin gajeren lokaci da kuma hanyoyin inganta ƙarfin tattalin arziki da warware rikice-rikice nan gaba. Wadannan na iya taimakawa wajen magance daukar 'yan kungiyar ta'adda da hana rikice-rikice tsakanin kabilu.

Hakazalika, ƙungiyoyin da aka ware da ma mutane a duk faɗin yankin - musamman waɗanda suke nesa da kujerun iko na ƙasa - suna buƙatar su ma a basudamar fadar ra’ayinsu game da yadda za a gudanar da iko kan su.

Dole ne gwamnatoci su kuma kare mutanensu. A duk lokacin da jami'an tsaro suka keta hakkin bil adama, suka ci zarafinsu, dole ne gwamnatoci su hukunta wadanda suka aikata hakan.

Zaman lafiyar Mali na da matukar muhimmanci ga yankin baki daya, in ji Sakatare Hale: “Muna yaba wa kudirin gwamnatin rikon kwarya na samar da shugabanci da ta dade ta na bukata, yaki da cin hanci da rashawa, da sake fasalin tsaro. Duk da haka, mun yi imanin cewa ya kamata a fara aiwatar da waɗannan gyare-gyare a yanzu kuma a miƙa su ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokiradiyya, gwamnati mai wakilci a cikin watan Afrilu na 2022, kamar yadda gwamnatin rikon kwarya ta amince. ”

Zahiri, gwamnatocin damokiradiyya sun fi dorewa,sina kuma tafiyar da komai a bayyane, da sadaukar da kai ga 'yancin bil adama, dacewar ci gaban tattalin arziki, da rashin fuskantar rikici-rikice, fiye da mulkin da ba na dimokiradiyya ba.

"Muna fatan ci gaba da aikinmu tare da abokan kawancenmu na Afirka da na Turai," in ji Sakatare Hale, "don taimakawa wajen samar da ci gaba da zaman lafiya a yankin na Sahel."

XS
SM
MD
LG