Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharhin Masana Kan Batun Girke Jami'an Tsaro a Majalisar Dokokin Najeriya


Jami'an Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya a Gaban Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja
Jami'an Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya a Gaban Majalisar Dokokin Najeriya a Abuja

A Najeriya masu fashin bakin al’amurran yau da kullum sun suna ci gaba da bada fassarar da bamdabam dangane da batun toshe kofar shiga majalisar dattawa da jami’an tsaro su kayi, wanda ya janyo korar babban darektan hukumar tsaron farin kaya na kasar Lawal Daura.

Masu sharhin sun bayyana cewa tun farko yadda aka kirkiro jam’iyyar APC daga jam’iyyu masu bambancin ra’ayi da kuma akida ya taimaka wajen rashin iya tafiyar da ayyukan gwamnati a siyasance.

Malam Zailani Baffa na Jami’ar Tafawa Balewa dake Bauchi, na ganin cewa salon da shuba Buhari ya dauka na kyale kowa yayi yadda ya ga dama shi ya samar da kafar da kadangare ya shiga.

Shi kuma malam Yusuf Abdullahi, na kwalejin kimiya da fasaha ya ce hadakar da aka yi tsakanin jam’iyyun a APC tun farko a jam’iyyar bai yi daidai ba saboda akidun su sun bambanta. Ya kara da cewa matakin kai jami’an tsaro na DSS majalisar bai dace ba, kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa a lokacin da jami’an tsaron suka toshe ginin majalisar ‘yan PDP ne kawai a wajen.

A nasa tsokacin shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin musulmai da kristoci, Ambasada Aminu Garba sidi, matakin da mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya dauka ya kare martabar dimokradiyya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG