Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shari'as Hosni Mubarak Ta Gamu Da Cikas


Tsohon Shugaban kasar Misira Hosni Mubarak lokacin da aka kawo shi kotu a kan gadon asibiti
Alkalin dake sauraron karar da aka shigar kan tsohon shugaban kasar Misira Hosni Mubarak ya maida shari’ar karkashin wata kotu.

An yanke wannan hukumcin ne ba da dadewa ba bayanda Mr. Mubarak dan shekaru 84 ya isa kotun dake birnin Alkahira yau asabar a kan gadon asibiti.

Za a sake wani zaman shari’a ne sakamakon daukaka karar da Mr. Mubarak yayi yana kalubalantar hukumcin daurin rai da rai da aka yanke mashi sabili da mutuwar daruruwan masu zanga zanga lokacin da ake zanga zangar neman canjin lamuran mulki.

An ba Mr. Mubarak izinin daukaka kara ne a watan Janairu bayanda wani alkali ya yanke hukumcin bara cewa, shi da tsohon ministan harkokin cikin gida na gwamnatinsa basu dauki matakin hana kisan kimanin masu zanga zanga dubu daya a shekara ta dubu biyu da goma sha daya, a zanga zangar da tayi sanadin hambare gwamnatinsa.

An tuhumi Mr Mubarak da wadansu mutane biyar da suka hada da mukarrabansa a shari’ar. Kotun daukaka karar kasar Misira ta bada izinin sake sauraron karar bisa ga bukatar da masu shigar da kara da kuma wadanda suke kare shi suka gabatar bayan korafin da aka yi cewa, shaidun da masu shigar da kara suka gabatar basu da tasiri.

Ana kuma tuhumar ‘ya’yan Mr Mubarak biyu Gamal da Alaa da laifin cin hanci da rashawa a wata shari’ar dabam.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG