Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shari'ar Manafort: An Yi Barazanar Kashe Alkali


Tsohon Ciyaman din Kwamitin Yakin Neman Zaben Trump, Paul Manafort.
Tsohon Ciyaman din Kwamitin Yakin Neman Zaben Trump, Paul Manafort.

A wani al'amari mai firgitarwa, Alkalin da ke shari'ar tsohon ciyaman din kwamitin yakin neman zaben Shugaba Donald Trump, Paul Manafort, ya ce an yi barazanar kashe shi.

Alkalin da ake shari’ar tsohon Ciyaman din kamfe din Shugaban Amurka Donald Trump wato Paul Manafort a gabansa, ya ce an yi barazanar kashe shi kuma yanzu haka ma wasu jami’an tsaro ne ke kare shi.

Alkalin Kotun Gunduma Thomas Selby Ellis ya gaya ma namena labarai jiya Jumma’a cewa, “duk inda na je, kafa ta kafar jami’an tsaro,” ya kara da cewa “kai, ko otal ma ba na iya zuwa ni kadai; ba na ma iya bayar da sunan otal din.”

Manema labarai sun bukaci alkalin ya gaya masu sunayen mambobin kwamitin taya alkali yanke hukunci, wato Juror, amma ya ki, ya na mai nuni da dalilai na tsaro. Alkali Ellis ya ce rayukan ‘yan kwamitin taya alkalin ma na iya shiga hadari muddun ya bayyana sunayensu, ya ce ya kamata ya kare “salamarsu da lafiyarsu.”

‘Yan kwamitin taya alkalin sun yi zama a karo na biyu jiya Jumma’a; yayin da Shugaba Trump ke bayyana shari’ar Manafort da “abin bakin ciki.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG