Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekara Daya Kenan da Rasuwar Gwamna Patrick Ibrahim Yakowa


Marigayi Ibrahim Yakowa gwamnan jahar Kaduna da ya rasa ran shi cikin hatsarin jirgin sama ranar 15 ga watan disamban shekarar 2012.

An yi bikin tunawa da marigayi Patrick Ibrahim Yakowa gwamnan jahar Kaduna da ya rasu bara a hatsarin jirgin sama a Najeriya

Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ya halarci bikin da aka yi don tunawa da gwamnan jahar marigayi Patrick Ibrahim Yakowa wanda Allah Ya yiwa rasuwa ranar goma sha biyar ga watan Disamban shekarar dubu biyu da goma sha biyu cikin wani hatsarin jirgin saman da ya faru a jahar Bayelsa. An yi bikin ne albarkacin cikon shekara daya da mutuwar gwamnan marigayi. Isah Lawal Ikara ya tattauna da uwargidan marigayin Mrs.Amina Ibrahim Yakowa wadda ta kara yiwa Allah godiya, kuma ta kara yabon marigayin wanda ta ce shekarun su talatin da hudu su na zaman aure kamar yadda za ku ji a cikin rahoton da ya aiko daga Kaduna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG