Accessibility links

Gwamna Murtala Nyako Yace PDP Bata da Hujjar Shigar da Wannan Kara

  • Aliyu Imam

Gwamnatin jihar Adamawa ta maida martani kan karar da uwar jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta shigar tana kalubalantar gwamnoni biyar da suka sake sheka.

Gwamnatin jihar Adamawa ta maida martani kan karar da jam’iyyar PDP mai mulkinn kasar ta shigar gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja, inda take neman kotu ta kwace kujerun gwamnonin nan biyar wadanda suka fice daga cikin jam’iyyar suka koma jam’iyyar hamayya ta APC.

A cikin rahotonda da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana, gwamna Murtala Nyako, ta bakin darektan yada labaransa malam Ahmed Sajo, yace ai PDP bata ta da hujjar shigar da wannan kara domin a baya taci gajiyar irin wannan mataki.

Gwamnonin da ake karar sune Murtala Nyako na jihar Adamawa, Rabi’u Musa Kwankwaso na jihar Kano, Abdulfatai Ahmed na jihar kwara, da Aliyu magatakarda wamako na jihar sokoto, da kuma Rotimi Ameachi na jihar Rivers.

A karar da babban lauya a Najeriya Alex Ezume ya shigar a madadin PDP, ya nemi kotun ta karbe mukaman ta mikawa mataimakan wadannan gwamnoni idan basu canza sheka tare da gwamnonin ba, domin kamar yadda yake cewa ai jam’iyya ake zabe ba mutane ba.

XS
SM
MD
LG