Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekau: Manazarta Na Tofa Albarkacin Bakinsu Kan Tukwicin $7m


Abubakar Shekau, a lokacin da ya ke magana gaban kamara cikin kwannakin baya.

A jiya ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi tayin dala miliyan bakwai ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Wannan tukwici na dala milliyan 7, wato naira biliyan 2.5 da gwamnatin Amurka ta yi tayinsa ga duk wanda ya ba ta bayanan da za su kai ga gano jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau, na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ke kara kaimi wurin kai hare-harenta.

Amurka dai ta saba gudanar da irin wannan shirin bada tukwici wanda ake kira “reward for justice” a turance, wanda ke bayar da miliyoyin daloli ga duk wadanda suka bayar da bayanan wasu ‘yan ta’adda da aka fitar da sunayensu ake nema ruwa a jallo.

A wannan karon, wannan shiri ya karkata ne ga Shekau.

Tun da Amurkar ta bayyana wannan tukwicin, manazarta a Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamarin.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wa wakilin Sashen Hausa, Hassan Maina Kaina ra'ayoyinsu kan wannan shirin a cikin wasu hirarrakin da ya yi da su.

Kwararre kan sha’anin tsaro, farfesa Muhammad Tukur Baba ya ce “dole mu yi murna cewa Amurka ta dauki Shekau ‘dan ta’adda wanda ya addabi duniya, ba Najeriya kadai ba.”

Manjo Janar Junaidu Sani Bindawa, wanda shi ne tsohon babban kwamandan runduna ta bakwai da ke yaki da Boko Haram, shi kuma ya ce a ganin sa zai yi wuya wannan tukwicin ya yi tasiri.

Shi ma, Farfesa Muhammad Tukur Baba, ya ce ta kowane fanni aka duba wannan al’amari tamkar taimako ne ga kasashen da Boko Haram ke addaba.

”Ta’addancin Boko Haram abu ne da ya shafi kowa a duniya, saboda haka wannan yunkuri na Amurka na nuna cewa lamarin ya dame ta ita ma.”

Wannan shirin na bayar da tukwici, na sirrinta bayanan duk wadanda suka tsegunta masa, har ma da bada kariya idan da bukatar hakan.

Kawo yanzu dai, ba a samu wanda ya fito da wasu bayanai kan Shekau ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG