Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rasha Ya Kai Ziyara Kasar Masar


Shugaban Rasha Vladimir Putin

A wni abun da ake ganin tamkar wani yunkuri ne na inganta dangantaka, shugaban kasar Rasha ya kai ziyara kasar Masar

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya fara rangadi na kwanaki biyu a Masar, ziyarar da yake yi da zummar inganta dangantaka tsakanin hukumomin kasarsa da kuma takwarorinsu dake Alkahira.

A jiya Litinin ne shugaban kasar Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya tarbeshi a babbar tashar saukar jiragen sama dake Alkahira.

Shugaban na Rasha shi ne shugaban wata kasa da ba ta Larabawa da yake goyon bayan shugaba Sissi, wanda ya fuskanci zazzafar tuhuma daga hukumomin Amurka saboda mummunar matakan da ya dauka na murkushe 'yan hamayya tun bayan da ya hambare shugaba Mohammed Morsi na kunigyar‘Yanuwa Muslim da sojoji suka yiwa juyin mulki cikin watan Yuli na 2013.

An kashe daruruwan magoya bayan Mr. Morsi, kana an daure wasu dubbai a wani matakin murkushesu tun bayan da aka hambare gwanatinsa.

A cikin wata sanarwa da fadar Kremlin ta shugaban Rasha ta bayar tace Mr. Putin da shugaban na Masar yau Talata ake sa ran zasu tattauna kan hali da ake ciki a Iraqi, da Syria, da Libya, da kuma kan rikicin Isra'ila da Falasdinu.

Ofishin shugaban Masar ya fidda sanarwar cewa shugabannin biyu zasu sanya hanu kan yarjejeniyoyi yau Talata, sai dai jami'an kasar basu bada bayani kan irin yarjejeniyoyin ba.

Ahalinda ake ciki kuma, jiya Litinin Masar ta dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa, ta kuma bada umarnin a gudanar da bincike kan mumunar tarzoma da ta auku a wani kauye tsakanin jami'an tsaro da kuma masu sha'awar kwallon kafa. Al'mari da ya halaka mutane fiyeda ashirin.

XS
SM
MD
LG