Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shimon Peres Na cikin Gaggan Mutanen Karni Na 20-Obama


Shugaba Obama a wurin jana'izar tsohon firayim ministan Israila
Shugaba Obama a wurin jana'izar tsohon firayim ministan Israila

Shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar da jawabin ban kwana a wajen shirin jana’izar tsohon shugaban Isra’ila Shimon Peres, inda ya bayyana shi a matsayin “daya daga cikin gaggan mutanen karni na 20.”

Obama ya kuma kwatanta marigayi Peres da fitattun mutane irinsu Nelson Mandela da Sarauniya Elizabeth ta Burtaniya tare da nuna farin ciki kan karramawar da aka mai.

“Ga jama’ar Isra’ila, ina so in ce wannan babbar karramawa ce, kasancewa ta a birnin Kudus, domin na yi ban kwana da abokina Shimon Peres, wanda ya nuna cewa adalci da sa buri, na daga cikin akidar Zionist mai kare muradun kasar Yahudawa, domin samun walwala a kasarsu.”

A farkon jawabinsa, shugaba Obama ya yi nuni da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, wanda ke zaune a sahun farko cikin bakin da suka halarta, inda ya jinjina zuwansa jana’izar ta Shimon Peres, ya kuma kara da cewa wannan wata alama ce da ke nuna cewa akwai bukatar a karafafa yunkurin samar da dawwamammen zaman lafiya.

Rabon da Shugaba Abbas ya halarci birnin na Kudus, tun a shekarar 2010, kuma shi ne na farko cikin shugabannin Larabawa da ya nuna alhininsa dangane da rasuwar Peres a ranar Larabar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG