Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske Gwamna Matawalle Ya Koma APC?


Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

Matawalle ya dare karagar mulkin jihar karkashin tutar jam’iyyar PDP, bayan da kotun koli ta soke nasarar da APC ta samu a zaben 2019.

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, Gwamna Bello Matawalle ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Bayanan sauya shekarar gwamna wanda ke wa’adin mulkinsa na farko na zuwa ne, bayan da daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook, wanda ke nuni da cewa Matawallen ya sauya sheka.

Zamfara ta dawo gida! Maraba Matawalle.” Mai baiwa Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya ce a ranar Lahadi.

Sai dai ba a ga wata sanarwa da jam’iyyar ko shi ofishin gwamnan ya fitar kan cewa ya koma jam’iyyar ta APC ba.

Amma dama an jima ana rade-radin cewa Matawallen zai koma jam’iyyar ta APC wacce idan hakan ta tabbata, za ta kasance tana da gwamnoni 20 cikin jihohi 36 da ke kasar.

Karin bayani akan: Bello Matawalle, APC, jihar Zamfara, jihar Cross River, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Tsohon hoto: Matawalle (hagu) da Shugaba Buhari (dama) (Facebook/Gwamnatin Zamfara)
Tsohon hoto: Matawalle (hagu) da Shugaba Buhari (dama) (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

A baya, gwamnan ya sha musanta rahotannin da ke cewa zai fice daga PDP.

Matawalle ya dare karagar mulkin jihar karkashin tutar jam’iyyar PDP, bayan da kotun koli ta soke nasarar da APC ta samu a zaben 2019.

A watan Mayu gwamnan jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya Ben Ayade, shi ma ya koma jam’iyyar ta APC daga PDP.

XS
SM
MD
LG