Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tababa Kan Shirin Gwamnatin Najeriya Na Sake Tsugunar Da Yan Boko Haram Da Suka Tuba


United Nations Secretary-General Antonio Guterres
United Nations Secretary-General Antonio Guterres

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi nuni da cewa gwamnati na yin wani shiri cikin sirri mai taken Sulhu, wanda aka tsara don fitar da kwamandojin kungiyoyin 'yan ta'adda, da suka hada da Boko Haram da ISWAP daga cikin dazuzzuka, gyara su da samar musu da sabbin hanyoyin rayuwa.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacinda hukumomin tattara bayanan sirri suka fara gudanar da bincike kan tubar da wasu 'yan ta'adda sama da 1,200 da iyalansu suka yi cikin makwanni uku da suka gabata.

Binciken dai kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, na neman tabbatar da shin da gaske mayakan sun tuba ne ko kuma dabara ce ta kara tsananta ayyukan ta'addanci a duk faɗin Najeriya.

Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Idan ana iya tunawa wasu shugabanni da al'ummomin yankunan Arewa maso gabas da ma sarakunan gargajiya, sun nuna rashin amincewarsu da sake shigar da tubabbun 'yan Boko Haram din a cikin al’ummansu.

A baya ma sai da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, su ma suka nuna damuwa kan cewa al'ummomin da 'yan ta'adda suka kashe dubban mutanensu da lalata musu dukiyoyi, ba za su yarda da kuma amincewa da wannan tubar ba.

Idan aka yi bita a kan yanayin da wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita suke ciki, da kuma rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar mai taken “The New Humanitarian” wanda ya ce gwamnatin Najeriya ta yi wani shiri a boye na magana da manyan mayakan da ke ikirarin jihadi a cikin daji don karfafasu su bar ayyukansu na ta’adanci ta hanyar amfani da makamai, dole ne al’umman su yi ta shakku kan gaskiyar lamarin yin tuba.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniyar dai ya yi binciken ne tsawon watanni shida kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

A yayin binciken, Majalisar Dinkin Duniya ta yi hira da jami'an gwamnati, tsoffin masu ikrarin jihadi, manazarta, 'yan jarida, mutanen da suka rasa muhallansu a bisa rikcin mayakan Boko Haram, da ma'aikatan kungiyoyin fararen hula, wadanda suka nemi a boye sunayensu ko a canzasu saboda halin tsaro kuma duk ba su gamsu da batun sake tsugunar da mayakan a cikin al’ummar da suka wargazar da rayukan su ba.

Haka kuma, wasu daga cikin wadanda aka zanta da su sun tabbatar da cewa rashin hukunta akasarin wadanda suka aikata ta’adi a yankunan Arewa maso gabas ya sanya al’umma cikin zaman dar-dar.

A wani bangare kuma, jami’an tsaro sun yi imanin cewa sulhu zai iya bude kofar yarjejeniyar zaman lafiya har ma ya kawo karshen tsaikon rikicin da yanzu aka kwashe sama da shekara goma sha biyu ana yi.

Saidai masana harkokin tsaro kamar su Kabiru Adamu na ganin cewa bai kamata a yi sulhu ga miyagun da ke kisa ba.

XS
SM
MD
LG