Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske ‘Yan Majalisu Na Shirin Tafka Magudi A Babban Zaben Shekarar 2023?


Majalisar Wakilan Najeriya
Majalisar Wakilan Najeriya

A ranar lahadi ne wasu masu sukar manufofin gwamnati suka fara tattaunawa kan wannan damuwar ta su a kafaffen sadarwa na zamani inda suka yi shelar cewa, 'yan majalisun tarayyar kasar na yunkurin tafka magudi a babban zaben shekarar 2023, ta hanyar yin kwaskwarima a dokar zabe ta shekarar 2021.

Akasarin masu fargabar sun fara magana ne ta kafoffin sada zumunta kamar su Tuwita sannan suka yi hira da wasu kafaffen yada labarai kamar su ThisDay inda suka ba da misali musamman da sashi na 50 sakin layi na 2 na daftarin kudurin na shekarar 2021, wanda yan majalisun kasar za su fara aiki a kai daga gobe talata, wacce suka ce za ta hana tattara sakamakon zabe ta yanar gizo.

Tun farko ma, an sami kungiyoyin fararren hula da aka fi sani da CSOs kimanin 22, suna bayyana damuwa game da shirin da 'yan majalisun dokokin kasar ke yi na zartar da kudurin zuwa doka ba tare da sanya bangaren tattara sakamakon zabe ta yanar gizo ba a ciki.

Kungiyoyin fararen hulan sun kuma yi ikirarin cewa tun da shugaba Muhammadu Buhari ba ya wani ja da su, 'yan majalisar suna aiki don cimma na su burin inda suka yi kira ga ‘yan kasar su yi tsayin data kan hana aukuwar lamarin.

Kungiyoyin fararren hulan da suka yi ikirarin sun hada da kungiyar YIAGA ta matasa masu neman ci gaba da yanci, kungiyar raya sabbin muryoyin matasa da ta shirya jagoranci a nahiyar Afurka wato MACAA, Cibiyar furta muryar jama’ar nahiyar Afurka da dai sauransu.

Da mu ka tuntubi dan majalisar tarayyar Najeriya kan lamarin, Hon. Yunusa Ahmad Abubakar, ya ce a kowanne lokaci kishin Najeriya su ke sanyawa a gaba, kuma za su yi duk mai yiyuwa wajen yin abin da ya kamata kan kudurin dokar zaben ta shekarar 2021.

Tun ba yau ba ne 'yan Najeriya ke ta fafutukar ganin an amince da batun tattara sakamakon zabe ta yanar gizo lamarin da wasu ke ganin zai tairnaka ga ci gaba a fannin zabe la'akari da yadda wasu matasa ke iya satar bayanai ko yin amfani da kafaffen yanar gizo don cusa ra'ayoyin bogi ko sakamakon zabe.

XS
SM
MD
LG