Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin EU Za Ta Cimma Matsaya Kan Tallafin COVID-19?


Da'irar da shugabbanin kasashen EU ke tattaunawa
Da'irar da shugabbanin kasashen EU ke tattaunawa

Shugabannin Tarayyar Turai sun yi hutu a safiyar yau Litinin a rana ta hudu da suke tattaunawa kan kokarin ganin an cimma wata matsaya dangane da COVID-19.

Mambobnin kasashen kungiyar tarayyar turai ta EU sun koma zaman tattaunawar da suke yi a kokarinsu na samar da kudaden tallafin da za su taimakawa yankin a yakin da ake yi da cutar coronavirus.

Tattaunawar ta su na da nasaba da kasafin kudi dala tiriliyan 2 da ake so a samar don da yaki da annobar.

Da tsakar ranar yau ake sa ran ci gaba da tattaunawar, wacce asali ya kamata a kammala ta a ranar Asabar.

Firayim Ministan Holland, Mark Rutte ya ce shugabannin na samun ci gaba a tattaunawar, sannan shugaban gwamnatin Austria Sebastian Kurz ya ce duk da cewa tattaunawar ta yi tsauri, “za mu kasance masu gamsuwa da sakamakon da zai bayyana a yau.”

Angela Merkel jim kadan bayan isowarta zauren tattaunawar
Angela Merkel jim kadan bayan isowarta zauren tattaunawar

A kwanakin da aka kwashe a wannan taro, an ga yadda kasashe mafiya karfin tattalin arziki da ke arewacin nahiyar turai, wato Austria, Denmark, Findland, Holland da kuma Sweden, suke sa-in-sa da takwarorinsu na kudanci, wadanda suka fi fuskantar matsalar ta coronavirus – suke kuma samun goyon bayan Jamus da Faransa.

Su dai kasashen na arewaci, suna so a saka matakan tsuke bakin aljihu a yarjejeniyar da za a kulla yayin da su kuma sauran kasashe irinsu Italiya da Spain suke so a sassauta matakan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG