Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Kira Matasan Gabashin Asiya Su Rungumi Yin Aiki


Shugaba Obama a Lao, gabashin Asiya
Shugaba Obama a Lao, gabashin Asiya

Yau Laraba shugaban Amurka Barack Obama ya gayawa gungun matasa daga fadin yankin gabashin Asiya, cewa ba zai wadatar ba suyi mafarki irin rayuwar da suke hankoro nan gaba,tilas su tashi "suyi aiki domin ganin sun cimma birunsu."

A wani taro da ya kunshi matsa da suke cikin shirin Mr. Obama ya kimtsa matasa, da ake kira YALI, shugaba Obama yace a duk tarihi matasa sune kan gaba wajen kawo canji da cigaba. Ya jaddada muhimmancin ganin kasashe sun inganta harkokin ilimi, kuma su tabbatar da cewa ci gaban da ake samu su hada harda 'yan mata, ba samari kadai ba.

Haka nan shugaban na Amurka yayi amfani da ziyarar da ya kai garin da ake kira Luang Prabang, wajen bayyana adawa ga ra'ayin cewa "Amurka ta maida hankala a kanta kadai" abun da Donald Trump yake tallatawa, da zargi kan kungiyar tsaro ta NATO, da kuma yunkurin gina ganuwa tsakanin Amurtka da makwabciyarta, wato Mexico.

Kodashike bai ambaci sunan Donald Trump ba, yace saboda girman Amurka sai tayu wasu Amurkawa zasu saki jiki su ce basa bukatar sanin wasu sassan duniya.

XS
SM
MD
LG