Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Sa Wasu Suke Neman Ballewa daga Kasashensu?


'Yan rajin neman kafa kasar Bifra daga Najeriya
'Yan rajin neman kafa kasar Bifra daga Najeriya

Rajin neman kafa sabbin kasashe na son zama ruwan dare gama duniya kama daga kasar Najeriya inda 'yan kabilar Igbo ke neman barin tarayyar Najeriya zuwa kasar Spain in 'yan Catilina har ma suka kada kuri'ar neman barin kasar su kafa tasu.

Rajin neman kakkafa sabbin kasashe na neman zama ruwan dare gama duniya.

To shin me ke sa wasu bangarori ke son ballewa daga kasashensu?

Masanin siyasar duniya Dr. Abbakar Umar Kari ya amsa wannan tambayar a hirar da yayi da wakilinmu, Hassan Maina Kaina, inda yake cewa “na farko akwai wadanda suka gaji da irin zaman da a keyi. Suna tunanen ko ana musguna masu ko kuma ana take masu hakinsu ko kuma akwai wasu bukatu da suke so kuma babu alamar cewa bukatun za’a biya masu.”

Shima Dr. Abubakar Sani Mabudin Borgu, shugaban kungiyar ‘yan kishin kasa ta “Think Nigeria First Initiative” yace ‘rashin kishin kasa na daga cikin abubuwan dake kawo korafe korafe da neman a raba kasa. Dr Kari yace wani lokacin ta kan kai yakin sunkuru kamar yadda ya faru a kasashen da Birtaniya.

Ko bayan Dr. Kari da Dr. Sani, wakilin namu ya jiyo karin fashin-baki daga wasu akan wannan batu.

Ga dai Hassan Maina Kaina da karin bayanin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG