Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Menene Sanadin Hatsarin Jirgin saman Rasha ?


Furanni da aka ajiye domin karramar mutanen da suka rasu a hadarin jirgin Rasha

Yayinda kwararru daga kasashen Rasha da kuma Misira suke gudanar da bincike domin gano masababin faduwar jirgin saman kasar Rasha ranar asabar da ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane dari biyu, Wani tsohon matukin jirgin sama a Najeriya ya yi tsokaci kan abubuwan dake haddasa haduran jirgi.

Kyaftin Mohammadu Bala Jibrin wani tsohon matukin jirgin sama a Najeriya ya bayyana cewa, kimanin kashi saba’in cikin dari na nadarin jirgin sama yana faruwa ne daga minti bakwai na farkon tashin jirgin, ko kuma minti bakwai kafin a sauka. Saboda haka yakan faru ne kusa da tashar jirign sama. Kasancewa wannan jirgin na Rasha ya gamu da hadari bayan kusan minti ishirin da uku da tashi, yana kusan kafa dubu talatin da daya a sararin samaniya, yasa ya fita daga matakin na farko na kasancewa kusa da tashar jirgin sama.

Wannan ya tabbatar da cewa, akwai babbar hujjar da ya sa jirgin ya fado daga sama. shaidun farko sun nuna cewa, jirgin ya tarwatse ne a sararin samaniya. Bisa ga cewarshi, akwai abinda ake kira “explosive decompression” wanda idan ta faru yakan haddasa tartwatsewar jirgi a sararin sama. Banda haka kuma ya faru a wani wurin da ake gani, mai yuwuwa ne wadansu abokan gaba suka kakkabo shi. Saboda haka bincike ne kadai zai tabbatar da ainihin abinda ya faru.

Yace idan dai har matukin jirgin ya iya tuntubar cibiyar kula da sufurin jiragen sama kafin aukuwar hadarin, zai nuna ke nan cewa, akwai wani abinda ya faru kafin jirgin ya tarwatse. Bisa ga cewarshi, akasarin haduran jiragen saman da aka samu a Najeriya sun auku ne galibi sabili da kura kuran da ma’aikata suka yi, kama daga kula da lafiyar jirgin da kuma yanayin sararin samaniya.

Ga cikakken bayanin da ya yiwa wakilinmu a shiyar Bauchi Abdulwahab Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG