Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin su wanene ke cikin sabuwar jam'iyyar PMP?


INEC, hukumar zabe wadda PMP ke neman ta yi mata rajista

Wadanda suka kafa sabuwar jam'iyyar People's Mega Party ko PMP a takaice sun ce zasu nemi yin rajista ta hukumar zabe kafin su bayya sunayen wadanda suka kafa jam'iyyar a fili

Sabuwar jam'iyyar PMP ko Peoples' Mega Party wadanda suka ki jinin shugabancin PDP da APGA ne suka fice suka kafata da niyar zuwa wurin hukumar zabe ko INEC ta yi masu rajista.

Haka nan ma sun yi ikirarin akwai wasu da APC da suka fusata da lamuran jam'iyyar tare da su a cikin sabuwar jam'iyyar PMP.

Shugaban jam'iyyar Chief Terry Okpara shi ne mai taimakawa tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara akan harkokin siyasa Barrister Ahmed Gulak.

Manyan 'yan PDP da ake raderadin suna cikin sabuwar jam'iyyar ba zasu fito fili ba siai jam'iyyar ta samu rajista ko kuma bayan saukan shugaban PDP na yanzu Sanata Ali Modu Sheriff nan da wata uku.

To saidai shi Ahmed Gulak da ake ganin yana kan gaba a sabuwar jam'iyyar ya musanta hakan. Yace babu hanunsa a ciki. Yace shi bai santa ba, bai kuma san lokacin da aka kafata ba. Yace baya ciki kuma bashi da niyar shiganta.

Shugaban amintattun PDP Sanata Walid Jibrin ya samu labarin neman kafa jam'iyyar lamarin da ya sa ya baiwa wadanda suka fusata hakuri. Yace duk abun da mutun ya yi cikin fushi ba zai doreba. Domin ba'a yiwa mutum dede ba sai ya fice ya kafa wata jam'iyyar!

Amma shugaban PDP Ali Modu Sheriff na cigaba da kira ga abokan hamayyarsa da aka tabbatar suna da hannu a sabuwar jam'iyyar da su janye da yin alwashin PDP din zata farfado.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG