Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Super Eagles Za Su Taka Rawar Gani a Rasha?


Wasan da Ingila ta lallasa Najeriya da ci 2-1 a karshen makon da ya gabata a filin Wembley

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Ingila ta doke 'yan wasan Najeriya na Super Eagles da ci 2-1 a wasan sada zumunci da suka buga a Wembley yayin da ake shirye-shiryen gasar cin kofin duniya a Rasha.

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya na gab da kammala wasanninta na sada zumunci, wadanda ta ke bugawa a matakin ta da tsimin tunkarar gasar cin kofin duniya a Rasha a wannan wata.

A jiya Asabar Ingila ta lallasa tawagar ‘yan wasan ta Najeriya da ci 2-1 a filin Wembley da ke birnin London.

A baya Najeriyar ta kara da Poland, Serbia da kuma Congo a wasannin na ta da tsimi.

Najeriyar ta doke Poland da ci 1-0, ta sha kashi a hannun Serbia da ci 2-0 ta kuma yi kunnen doki da Congo inda aka tashi da ci 1-1.

Wasan da za ta yi nan gaba shi ne da Czech Republic, wanda shi ne wasan sada zumunci na karshe da za ta yi kafin danganawa da Rasha.

Najeriya na rukunin “D” da ke dauke da Crotia, Argentina da Iceland a gasar cin kofin na Duniya wanda za a fara ranar 14 ga watan nan na Yuni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG