Accessibility links

Sabili da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya taba ficewa daga jam'iyyar PDP amma daga bisani ya dawo shi ya sa jam'iyyar tana ganin fitar da ya sake yi yanzu tamkar ya je hutu ne, wato zai sake dawowa.

Lokacin da yake karbar katin zama dan jam'iyyar APC a Jada garinsa, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya mayarwa jam'iyyar PDP martani da cewa ba zai sake komawa jam'iyyar ba.

Ya ce PDP ta daina sauraren jama'a. Ta yi nisa bata jin kira. Tun da kuma bata jin kira me za'a yi da ita? Ya ce a yi watsi da batun PDP cewa shi Atiku Abubakar zai koma cikinta.Ya ce maganar banza ce.

Shi ma gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da ya canza sheka daga PDP zuwa APC ya garzaya garinsa Mayo Belwa domin karbar katin zama dan APC. Ya ce ya karbi katin APC wanda hakan ya nuna cewa PDP ta mace. Ya ce duk wani mutumin kirki a Najeriya idan yana son ya yi siyasa tsakaninsa da Allah ya shiga APC.

A wani halin kuma 'yan jam'iyyar PDP sun ce su basu razana ba da tagomashin da APC ke samu yanzu. Alhaji Yayaji Gombe wani jigo a jam'iyyar ya ce babu abun da APC zata yiwa PDP a faggen siyasa. Mahimman mutane sun riga sun sani cewa wadanda suka yi hadaka babu inda zasu je. Ya ce a jira nan da watanni biyu APC zata fashe ta lalace fiye da yadda ake tsammani.
XS
SM
MD
LG