Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Yaushe Za a Bude Sufurin Jiragen Kasa-da-Kasa a Najeriya?


Wani jirgin sama a kasar Ingila

Ministan harkokin sufurin sama, Hadi Sirika ya musanta matakin fara zirga-zirgar jiragen kasa-da-kasa a watan Oktoba kamar yadda jaridun kasar suka rawaito.

Ya bayyana cewa zasu bayyana lokacin da suka tsara fara fita da jirage.

Sirika ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa wata kila ma a fara zirga-zirgar jiragen kafin watan Oktoba.

Hakan na nufin cewa jirage masu aiki na musamman da na jami'an difilomasiyya ne kadai aka baiwa dama a halin yanzu, har sai an tabbatar da lokacin bude zirga-zirgar kasa-da-kasa.

A cikin watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa-da-kasa domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG