Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Gwamnatoci Na Ciyar Da Mabukata A Wata Ramadan Ta Cin Karo Da Kalubalen Zargin Almundahana


Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Yayin da al’umar musulmi ke daf da kammala ibadar Azumin Ramadana, aiwatar da shirin gwamnatoci na ciyar da mabukata a cikin wannan wata na cin karo da kalubalen zargin almundahana, inda ake tuhumar wasu daga cikin Jami’an gwamnati da hannu.

KADUNA, NAJERIYA - Irin wannan zargi dai ya sanya gwamnan jihar jigawa Umar Namadi dakatar da guda daga cikin kwamishinonin sa tare da bada umarnin gudanar da binciken kwakwaf.

Cikin wata sanarwa a jiya wadda sakataren gwamnatin Jigawa Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman Umar Namadi ya bada umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Aminu Kanta saboda zarginsa da hannu wajen almundahanar a tsarin aiwatar da Shirin gwamnatin jihar na ciyar da mabukata a wannan wata na Ramadana.

Comrade Salisu Mazge Gumel guda cikin jagororin kungiyoyin ci gaba da al’uma a Jigawa yana bibiyar yadda gwamnatin jihar ta Jigawa ke aiwatar da wannan Shirin na ciyarwa, la’akari da daruruwan miliyoyin naira da gwamnatin ta kebewa tsarin.

“Akwai kumbaya-kumbiya a cikin harkar, yanzu zaka baiwa mace yake kwano goma, Gero kwano 10, shinkafa kwano 10, amma bAbu wanda zai tsaya ya tabbatar da cewa, wannan adadi an dafa shi, baya ga haka ‘yan kwangilar dake rarraba kayan ga masu dafawar babu wanda zai sanya masu idanu ya tabbatar da cewa, ya bada adadin daya kamata ya baiwa masu dafawa.”

A jihar Kano ma dake makwaftaka da Jigawan, irin wannan badakala gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf ya gano a tsarin ciyar da mabukata na gwamnatin sa a cikin wannan wata mai alfarma.

Kimanin naira biliyan biyu gwamnatin ta kebewa shirin, amma a wata ziyarar ba zata gwamnan ya nuna rashin gamsuwa da nau’in abincin da ake baiwa talakawa.

Sanusi Bature Dawakin Tofa shine Daraktan yada labaru na gwamnan yace, “Mai girma gwamna ya kewaya da kansa daya daga cikin cibiyoyin da ake wannan aiki kuma ya ga abin da akeyi ya saba da umarnin daya bayar, wanda haka ta sanya ya bada umarnin cewa, tilas ne a canza wannan tsari kuma ayi bincike domin daukar mataki.”

Yanzu dai kusan makonni biyu kenan da suka shude amma har yanzu babu labarin dangane da irin matakin ladaftarwa da gwamnan ya dauka akan wadanda yace suna yi masa zagon kasa.

Dr Kabiru Sa’idu Sufi, mai sharhi akan harkokin gwamnati da lamuran yau da kullum yace, “Wannan yana nuna ta’azzara ne na cin hanci da rashawa da almundahana, musamman akan abubuwan da suka shafi ayyukan gwamnati.”

Wannan zargin almudahana a tsakanin Jami’an gwamnati na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya kef ama da kalubalen tsadar rayuwa a fadin kasar.

A saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Shirin Gwamnatoci Na Ciyar Da Mabukata A Wata Ramadan Ta Cin Karo Da Kalubalen Zargin Almundahana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG