Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Magance Matsalolin ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya


Bukin Bude Sabbin Hanyoyi A Jihar Adamawa

Gwamnatin tarayya da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross da kuma jami’ar Amurka a Najeriya, zasu fito da wani shirin magance matsalolin ‘yan gudun hijira a arewa maso gabas da zai samar da wata kafa don aiki tare da ‘yan gudun hijiran wajen shawo kan matsalolinsu na yau da kullum.

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya furta haka ne a jawabinsa na kaddamar da hanyoyi dari da bakwai masu nisan kilomita dari da sittin da tara a fadar jihar Adamawa da kuma yankunan da Boko Haram suka lalata. Ya ce da alamu hakar gwamnatin Buhari na cimma ruwa a yaki da cin hanci, samarwa matasa ayyukan yi da kawar da talauci.

Farfesa Osinbajo, ya ce tare da hadin gwiwar kungiyar da jami’ar gwamnati za ta kafa asusun da zai taimaka wajen sake sugunar da su da kuma ba su damar soma sana’o’in da ‘yan gudun hijiran za su dogara da su wajen biyan bukatunsu.

Bukin Bude Sabbin Hanyoyi A Jihar Adamawa
Bukin Bude Sabbin Hanyoyi A Jihar Adamawa

Gwamna Mohammed Umaru Jibirilla na jihar Adamawa ya ce shimfidar da gwamnatinsa ta yi na raya jihar itace ta dinke bambanci da ke sakanin al’umomin dake jihar mai kabilu tamanin da bakwai da addinai ma bambanta.

Shima da yake jawabi a bukin kaddamar da hanyoyin ministan raya birnin tarayya Abuja Alhaji Mohammadu Bello Musa, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta maida wa jihar Adamawa kudaden da ta kashe musammam wajen sake gina yankunan da rikicin Boko Haram ya daidaita, daga asusun da ta ware na sake gina arewa maso gabashin Najeriya.

‘Yabon na gari ya zamo tilas’ inji shugaban jam’iyar SDP ta jihar Adamawa Mallam Ibrahim Bebetu, ‘daya daga cikin jam’iyun adawa idan aka yi la’akari da ci gaban da jihar ta samu ta fannin gina hanyoyi, a hirar da Muryar Amurka ta yi da shi da yake magana kan yadda jam’iyarsu ke kallon kamun ludayin gwamnan jihar Adamawa Jibirilla.

Domin karin bayani saurari rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

DOMIN KARIN BAYANI

Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n

Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG