Accessibility links

Shirin Rage Fatara na Man Fetur a Jihar Adamawa


Wani matashi ke nan yayin da suke zanga-zanga

Shirin rage fatara na man fetur ya soma haifar da mai ido a jihar Adamawa inda fiye da matasa dubu uku suka samu aikin yi. Sai dai duk da nasarar da jihar ke ikirarin samu akwai korafe-korafe

Shirin rage fatara na man fetur ya soma haifar da da mai ido a jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi talatin da shida na Najeriya.

Idan aba'a manta ba a shekarar 2012 ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta janye tallafin kudin man fetur da 'yan kasan ke saya. A wannan lokcin kudin mai sai ya yi tashin goron zabi inda kudin galan daya ya tashi daga N260 zuwa fiye da N600.

Lamarin shi ya kai ga wata muguwar zanga-zanga na ma'akata gaba daya. Kasar ta shiga cikin wani rudani da tashin hankali da cece-kuce. Sai da gwamnati ta yi sassauci kafin a samu zaman lafiya. Sanadiyar tashin hankalin ya sa gwamnati ta fito da wani shirin rage zafin fatara da talauci da ragowar tallafin da ta janye. Musamman shirin ya tanadi samar ma matasa aikin yi domin a karkata hankulansu daga shiga tashin-tashina.

A jihar Adamawa da alamu kwaliya ta soma biyan kudin sabulu. A karkashin shirin na rage fatara fiye da matasa dubu uku aka dauka aiki. Wasu an koya masu aikin dubagari domin tsaftace muhallan jihar. Wasu sun koyi aikin dogarawan hanyoyi domin kiyaye zaman lafiya. Wasu kuma an koya masu sana'o'i daban-daban da nufin su yi aikin kansu da kansu tare da yin anfani da jari da aka basu.

Sai dai duk da wannan nasara da gwamnatin jihar ke ikirarin samu wasu suna korafin cewa gwamnati na nuna wariya game da wadanda aka dauka ko aiki ko koyon sana'a. Sun ce ba'a daukan matasan da basu da galifu, wato basu da wadanda zasu kama kafafunsu domin a daukesu.

Jami'in kula da shirin ya musanta zargin yayin da wakilinmu ya yi masa tambaya. Haka ma gwamnan jihar Murtala Nyako ya ce babu nunin wariya. Ya kara da cewa gwamnatinsa ta sha alwashin samar ma duk matasan jihar aikin yi.

Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG