Gwamnatin jihar Filato ta ce ta gano wata hanya ta magance barazanar tsaro, wacce za ta rika saka al'ummomi a harkokin tsaro.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya fada a taron da gwamnonin shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya suka gudanar a Lafiya, fadar jihar Nasarawa, cewa aiwatar da wannan shiri, wanda ake kira "Community Policing," zai taimaka wajen ba kowa dammar sa ido a harkokin tsaro.
Lalong ya ce za su farfado da shirin ayyukan rundunar tsaro ta "Operation Rainbow," dan 'yan sintiri, domin cimma matsalar tsaro.
Alhaji Ibrahim Yakubu Iro, Daraktan kungiyar Fulani da ke hankoron zaman lafiya da adalci a Najeriya, ya ce zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki zai taimaka.
Shugaban kungiyar matasan Aten na Kasa, Song Muru, ya ce, duba da matsalar karancin jami'an tsaro a kasa, ya zama dole gwamnati ta hada kan al'uma don samar da tsaro.
Jihar ta Filato ta sha fama da matsalolin tsaro masu nasaba da rikice-rikicen addini da na kabilanci, musamman tsakanin makiyaya da manoma.
A saurari rahoto cikin sauti daga jihar Filato.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 08, 2021
Ranar Mata Ta Duniya: Mata A Jihar Borno Na Neman Dauki
-
Maris 08, 2021
Mata Suna Neman Gwamanati Ta Dama Da Su
-
Maris 07, 2021
Ba Bu Wanda Yake So Najeriya Ta Rabu - NOA
Facebook Forum