Accessibility links

Shawarar da wani kwamiti a zauren babban taro na kasa yake tunanin gabatarwa kan soke tsarin kananan hukumomi daga matakan mulkin Najeriya ya harzuka kungiyoyin ma'aikatan kananan hukumomin

Kudurin da shugaban Kwamitin Hadin Guiwa Kan Rabon Ikon Shugabanci a zauren babban taro na kasa a Abuja, Ike Nwachukwhu, ya gabatar kan soke tsarin kananan hukumomi a Najeriya yana neman tayar da kura sosai.

Kudurin na Nwachukwu yace za a iya barin kananan hukumomi a Najeriya, amma kuma a ciore su daga matakan ikon kasa, ma'ana daga gwam,natin tarayya sai na jihohi kawai. Wannan yana nufin cewa ba za a gudanar da zabubbukan kananan hukumomi ba, haka kuma ba za a tura kudi kai tsaye ga kananan hukumomi su 774 dake cikin tsarin mulkin kasa ba.

Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta Najeriya, Comrade Ibrahim Khalil, wanda wakili ne a zauren taron na kasa, yayi watsi da wannan kuduri na Ike Nwachukwu, yana mai cewa su na magana da 'yan kwamitin a kan su duba irin abinda ya kira tu'annatin da gwamnoni suke yi ma kananan hukumomi tun maido da mulkin dimokuradiyya a 1999.

COmrade Khalil yace har yanzu akwai gwamnoni da yawa da ba su gudanar da zabubbukan kananan hukumomi ba, kuma a wuraren da aka yi din ma, gwamnonin ba su kyale su da su gudanar da ayyukan da suka tsara gudanarwa da jama'a.

Yace don haka ne zasu yaki wannan abu, tun daga cikin kwamitin har zuwa cikin zauren taro idan ya samu fita zuwa cikin zauren. Haka kuma yace zasu mike tsaye da kyamfe domin tabbatar da cewa ba a sukurkuta tsarin kananan hukumomin wadanda sune suka fi kusa da jama'a ba.
XS
SM
MD
LG