Accessibility links

Biyo bayan tabarbarewar tsaro a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar inda rigingimun ta'addanci, da kabilanci, da Fulani makiyaya da manoma, fashi da makamai da batutuwa da dama, shugaban Najeriya ya gudanar da taro da shuwagabbannin al-umma domin samo hanyoyin warware wadannan matsalolin.

A yammacin Alhamis dinnan ne a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja, aka kawo karshen taron da aka yi tsakanin shugaban kasa Goodluck Jonathan da gwamnonin kasar, da shuwagabannin hukumomin tsaro, da shuwagabannin addinai, inda aka duba hanyoyin da suka kamata a bi, da matakan da suka kamata a dauka, domin tabbatar da cewa an kawo zaman lafiya, tare da yaki da ta’addancin da ya bazu a duk fadin Najeriya.

Bayanan da suka fito a karshen taron sun nuna cewa taron ya amince bisa ga manufa, lallai ta’addancin dake wakana a cikin Najeriya a yanzu, bashi da wata nasaba da addinin Islama, sannan kuma daga yanzu za’a fara sa ido, da kayyade yadda masu wa’azi zasu ringa aikinsu, domin tabbatarwa ba’a yi amfani da addini ba wajen yada wasu manufofi da suka saba ka’idoji da aka san wadannan addinai na kawo zaman lafiya a cikin duniya ba.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi karin bayani akan sakamakon taron wanda suka shafe wuni daya sune yinshi a fadar shugaban kasa dake Aso Rock.
“AlhamdulilLahi zance, wannan taro yayi kyau kwarai da gaske, domin an fahimci cewa ta’addanci wanda yake faruwa a kasarnnan, soja ko police su kadai baza su iya maganinsa ba. Dole sai an hada da masu mulki na farar hula, da sarakuna da talakawa, ta nan ne kawai idan an hada kai wuri daya za’a cimma wannan abun”, a cewar Dr. Ganduje.

Sai dai taron bai kuduri yin sulhu da kungiyar tayar da kayar baya ba, da aka fi sani da Boko Haram.

Mr. Ganduje ya kara cewa “tattaunawa da ‘yan boko haram ma, wannan babu wanda ya kawo shi. Kuma sauran abubuwa dai wadanda za’a kawo su, abubuwa ne wanda bai kamata a fada a radiyo ba.”

“Akwai sabon salo da za’a fito da shi, batun yaki wannan baza a ajje shi, dole sai anyi amfani da makamai. Amma kuma akwai sabbabin hanyoyi na samun labarai da kuma hikimomi daban-daban wadanda za’a fito da su,” a karin hasken da mataimakin gwamnan jihar Kanon yayi.

Yanzu dai ‘yan Najeriya sun zuba idanu su ga irin tasirin da wannan taron zai yi, da kuma duba hanyoyin da shuwagabannin tsaro na Najeriya zasu yi amfani da damar da suke da ita, wajen tabbatarwa an samu nasarar wannan yaki da aka daura da ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram, da ma sauran kungiyoyi wadanda ke tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na Najeriya.

Wannan dai yana kasancewa ne bisa ga amincewar da taron yayi cewa za’a yi amfani da duk ‘yan Najeriya baki daya, kowa ya bada gudunmuwa domin tabbatar da cewa an yaki wannan matsala wadda aka tabbatar cewa jami’an tsaro kawai baza su iya yaki da ita ba.
XS
SM
MD
LG