Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Trump Na Korar Bakin Haure Bai Kankama Ba


Wasu jami'an tsaro suna tisa keyar wani bakin haure da suka kama

Babu wata alama da ta nuna a zahiri cewa an kaddamar da samamen kama bakin hauren da yawansu ya kai dubu 2,000 da ke zaune a nan Amurka ba bisa ka’ida ba, wadanda ake nufin mayar da su kasashensu na asali.

A jiya Lahadi hukumomin Amurka suka bayyana cewa za su kaddamar da samamen na cafke bakin hauren.

Mukaddashin hukumar shige da fice da kuma ta Kwastam, Chief Matt Albence ya ce, “akwai rukunin mutanen da muke kaikaita wadanda kotun shige da fice ta saurari kararrakinsu kuma alkali ya ba su umurnin su fice daga kasar.”

Sai dai bai ba da cikakken bayanin kan inda aka yi kamen ba ko kuma mutane na wa ake tsare da su.

Amma fargabar da bakin haure ke ta nunawa na kai samame gidajensu a manyan biranen kasar ba ta bayyana ba, domin ba a ga jami’an tsaron suna fasa kofofin gidajen bakin hauren suna kama su ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG