A yau Litinin, lauyoyin Fadar White House ke shirin mika hujjojin da za su kare Shugaba Donald Trump a shari’ar da Majalisar Dattawan kasar za ta fara saurara, kan shirin tsige shi daga mukaminsa.
Hakan na faruwa ne kwana daya gabannin a fara sauraren karar a gaban Majalisar.
A wani takaitaccen martanin farko kan tuhume-tuhumen da Majalisar wakilai ta amince da su a baya, Lauya Pat Cipollone da Jay Sekolow sun nemi ‘yan majalisar dattawan su yi watsi da tuhume-tuhumen da ake wa Trump saboda a cewarsu, “za su iya zama hadari ga kundin tsarin mulkin Amurka tare da yin mummunar tasiri ga tsarin gwamnati.”
Lauyoyin sun kuma kalubalanci majalisar wakilai akan cewa ta na kokari ta rage karfin ikon shugaban, dangane da damar da doka ta ba shi game da manufofin kasashen waje.
Sun kuma kara da cewa, majalisar ta wakilai, na kokarin hukunta bangaren zartarwa ne, saboda ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi na gudanar da ayyukansa.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka
Facebook Forum