Yayin da zabukan da za a yi a Nijeriya ta 2015 ke kara karatowa, ana kara samun takaddama tsakanin ‘yan jam’iyyar PDP mai mulkin Nijeriya da kuma ‘yan babbar jam’iyyar adawa ta APC, inda kowacce ke zargin dayar da shirin yin magudi da sauran halayya marasa kyau.
A wurin wani gangamin tallata dan takarar gwamnan jihar Adamawa karkashin PDP, Malam Nuhu Ribadu da Mataimakinsa Rev. Habila Istifanus, Nuhu Ribadu ya ce da jama’a su ne nasu don haka a masu addu’a. Shi ma wani jigon PDP din mai suna Santa Sale Zangina, ya kwatanta PDP da jirgin Nuhu mai dauke da kowace irin halitta.
To saidai su ma ‘yan APC sun yi nasu gangamin na mai da martani, inda wani jigon jam’iyyar mai suna Alhaji Abdurrahman Abba Jimeta, ya yi kashedin cewa, kamar yadda ‘yan PDP su ka maida magudin zabe tamkar shi ne Allahnsu, su kuwa a APC sun shirya ma mutuwa a yinkurinsu na kare kuri’unsu. Ya ce don haka duk wanda ke son shiga kabari da wuri to ya shirya yin magudi. To saidai kuma wasu ‘yan Mubi na cewa muddun ba a kare Maiha da sassan Mubi ba to lallai kam ba za su yi zabe ba.