Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Alassane Ouattara Na Ci Gaba Da Ziyara A Kasar Ghana


Shugaban Kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara ya kai ziyarar aiki a kasar Ghana, Shugaba Alhassan Watara ya samu kykkywar tarbo inda aka zagaya da shi cikin birnin kasar, Jama’a da dama sun fito sunyi Marhaba domin karbar Shugaban.

Shugaba Alassane Ouattara da Nana Akufo-Ado na kasar Ghana, sun gana a sirince. Shugaban kasar Ghana yayi godiya da amsar goron gayyata da shugaba Akufo-Ado yayai, ya kuma yi bayanin cewa kasashen biyu zasu samu Alkhairi da dama bayan sakamokon hukuncin kotu na kasa da kasa na shari’ar ruwan teku.

Shugaban Ghana ya jinjinawa bakon nasa shugaba Ouattara akan dattaku da ya nuna bayan bayyana sakamokon shari’ar, Ya kara da cewa a yayin shari’ar sun fahimci cewa sun shiga mawuyacin hali tsakanin su da Cote d’Ivoire, amma sun yi amfani da wannan a matsayin ginshikin kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A bangaren shugaba Alhassan, kuma ya nuna matukar godiyarsa ga shugaban kasar na Ghana game da wannan gayyata da kuma nuna godiyar sa musamman kan yadda kasar ta Ghana ta karbi ‘yan gudun hijirar kasar Cote d’Ivoire, a yayin da kasar ta shiga wani hali a kawanakin baya.

Kasashen biyu dake gaba wajan noman koko, a duniya sun kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa da zata basu damar cin gajiyar zufar su.

Dag Ghana ga rahoton da Ridwan Abbas ya aiko mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG