Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Laiberia ta Sanar Jiya Lahadi Zata Gudanar da Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu


George Weah dan takarar dake kan gaba yana kada kuri'arsa a zaben shugaban kasar Liberia

Bayan an kammala kidayar kashi 95 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Liberia makon jiya, Weah ya samu kashi 39% yayinda mataimakin shugaban kasar, Boaki ya samu kashi 29% ke nan babu wanda ya samu kashi 51% saboda haka za'a gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin 'yan takarar biyu

Za a gudanar da zagaye na biyu a zaben Shugaban kasar Liberiya, a tsakanin shahararren tsohon dan wasan kwallon kafan nan George Weah da kuma Mataimakin Shugaban kasa na yanzu Joseph Boakai, a cewar Hukumar Zaben Kasar a jiya Lahadi.

Bayan kidaya wajen kashi 95% na kuri'un da aka kada a wannan kasa ta Yammacin Afirka, Weah ya samu kashi 39% a yayin da shi kuma Boakai ya samu kashi 29.1%. Wannan na nuna cewa ke nan babu daya daga cikinsu da ya sami adadin da ake bukata na kashi 50% kafin a zama Shugaban kasa, a zagaye na farko na zaben na makon jiya.

Masu zabe miliyan 2.1 da su ka yi rajista a kasar ne suka kada kuri'ar zaben wanda zai gaji Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da ta zama Shugabar kasa a Afirka, wacce za ta sauka bayan ta ciki wa'adi biyu masu tsawon shekaru shida-shida, kamar yadda kundin tsarin mulkin Liberia ya tanada.

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG