Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Daura Damarar Sake Tsayawa Takara


Buhari A Yayin Da Ya Mika Takardar Tsayawa Takara
Buhari A Yayin Da Ya Mika Takardar Tsayawa Takara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mikawa shelkwatar jam’iyyar APC takardar sa ta tsayawa zaben fidda gwani don neman tazarce a 2019.

An yi dafifi a shelkwatar don shaida mika takardar inda hakan ya hadu da mika takardun da wasu masu neman takara na sauran kujeru kamar gwamna da majalisar tarayya.

Shugaban jam’iyyar Adams Oshimohle, ya jagoranci sauran shugabanni don karbar takardar da magoya baya su ka tara Naira miliyan 45 su ka sayawa shugaba Buhari.

Wani fitaccen dan siyasa da ke mara baya Alhaji Sanin Malam, ya ce hanya daya mafi sauki ta nasarar APC a dukkan matakai itace ta fidda gwani da amfani da tsarin ‘yar tinke.

Anguwar Wuse 2 inda sakatariyar APC ta ke na samun cunkuson motoci,yawan motocin jami’an tsaro da ya hada da datse hanyoyin yankin lokacin da shugaba Buhari yakai shiga sakatariyar.

Domin karin bayani, saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya...

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG