Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnonin APC


Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a fadarsa dake birnin Abujan Najeriya

Bayan taron bayanai sun nuna cewa taron an samu gagarumar nasara ta gasken gaske.

Gwamnonin sun yi tayin cewa zasu shiga tsakanin fadar gwamnati da majalisun dokokin kasar da zummar kawo karshen rigingimun dake tasowa tsakaninsu. Ta kuma dubu hanyoyin da za'a inganta muamala tsakanin shugaban kasa da gwamnoni.Gwamnonin sun kuma nemi a biya duk basuka da bukatun da gwamnonin ke dashi a fadar gwamnatin tarayya,

Malam Garba Shehu kakakin shugaba Buhari yace taron, kamar yadda suka yanke shawara, za'a dinga yinsa a kai a kai domin tuntubar juna da ba juna shawara da fadakar da juna akan duk abun da ya shafi kasa da harkokin mulki. Su gwamnonin suna fama da matsaloli da dama. Misali, jihohi da yawa suna bin gwamnatin tarayya bashi. Sun yiwa gwamnatin tarayya ayyuka da dama da aka ce za'a biyasu amma har yanzu shiru ka ke ji. Yanzu gwamnatin tarayya ta amince ta fara biyan kashi hamsin na basukan cikin gaggawa.

Dangane da jihohin da ba na APC ba ne, gwamnonin sun bukaci a yi adalci. A ba kowace jiha hakkinta, kada a ba kowace jiha fifiko.

Haka ma za'a kawo sasantawa tsakanin majalisar zartaswa da majalisar dokoki. Shugaban kasa ya yi na'am da yunkurin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG