Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari Zai Zo Ganawa da Shugaban Amurka


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Sabon shugaban Najeriya zai gana da shugaba Barack Obama na Amurka a wata mai zuwa domin tattauna yaki da kungiyar Boko Haram da wasu muhimman batutuwan.

A yau alhamis fadar White House ta ce Mr. Obama zai karbi bakuncin shugaba Muhammadu Buhari a ranar 20 ga watan Yuli.

Wata sanarwa ta ce shugabannin biyu zasu tattauna yadda zasu karfafa dabarar yakar Boko Haram ta fannoni dabam-dabam kuma da hadin kan yankin; da kuma wasu muhimman sauye-sauyen tattalin artziki da siyasa a Najeriya. Manyan mashawartan shugaba Buhari zasu gana da takwarorinsu na Amurka a wani gefen.

A watan da ya shige aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari kan wannan kujera a bayan da ya kayar da Goodluck Jonathan a zaben da aka yi a watan Maris.

Shugaba Buhari ya lashi takobin murkushe zarmiya da cin hanci da kuma kawar da ‘yan Boko Haram wadanda suka kasha dubban mutane tun da suka fara tayar da kayar baya a 2009.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG