Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kara Ma Hafsoshin Soja Wa'adin Aiki


Shugaba Buhari tare da manyan hafsoshin sojan kasar da ministan tsaro a wajen wani buki a Jihar Zamfara

A bayan nazarin irin ayyukan sojan da ake gudanarwa yanzu haka a fadin Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari, ya yanke shawarar kara ma shugabannin rundunonin sojan kasar wa'adi a kan mukamansu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa rundunonin sojin kasar wa'adi akan mukamansu.

Wani mukarrabin shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa karin wa'adin aikin, ya shafi babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin; da babban hafsan rundunar sojojin kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai; da babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Marshall Sadiq Abubakar; da kuma babban hafsan rundunar mayakan ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas.

Idan ba a manta ba, an fuskanci rashin sanin tabbas a bayan da wa'adoin hafsoshin ya cika a wannan wata na Disamba, bayan da suka samu karin wa'adin tun farko a watan Disambar bara. A bisa tsarin aikin na soja, wa'adinsu ya kamata ya kare a watan Yulin da ya shige ne.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG