Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Karbi Takardar Shaidar Lashe Zabe Karo Na Biyu


An Baiwa Buhari Da Osinbajo Shaidar Lashe Zabe
An Baiwa Buhari Da Osinbajo Shaidar Lashe Zabe

Takaitaccen taron mika takardar shaidar lashe zaben 2019 da shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmud Yakubu ya mikawa shugaba Buhari don fara wa’adi na biyu, kuma na karshe a tsarin dokokin Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban dai wanda ya godewa magoya bayan sa, ya kuma yi sauri ya bukaci gujewa murnar da ta wuce kima ko habaici ga abokan hamaiya.

Hakanan ya zaiyana zaben a matsayin wanda a ka yi gudanar cikin adalci, inda ya ba da tabbacin ci gaba da aikin yaki da cin hanci da sauran alkawuran kamfen.

Shugabannin APC, ‘yan majalisar dokokin tarayya da manyan magoya baya su ka rufawa shugaban baya a taron.

Sakataren APC Mai Mala Mala Buni ya zaiyana lashe zaben a matsayin gagarumar nasara ga masu son sauya akalar mulki daga ‘yan jari hujja zuwa talakawa.

Jim kadan bayan kammala wannan taro ita ma PDP ta gudanar da taro inda ta yi watsi da sakamakon zaben.

Nan ma dan takarar PDP Atiku Abubakar ke kin amincewa da sakamakon da zaiyana cewa ko a gwamnatin soja ba a taba gudanar da zabe marar kan gado irin wannan ba.

Atiku ya yi ikirarin cewa daga sanar da sakamakon, Najeriya ta yi asarar Naira biliyan 85 daga masu zuba jari.

Jam’iyyar PDP ta ce za ta sanar da matakan da za ta dauka a gaba da kira ga magoya bayan ta su kwantar da hankalain su.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG