Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari ya kira kasashen Afirka su gaggauta cudanyar harkokin kasuwancin


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da na Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da na Kenya Uhuru Kenyatta

Jiya a birnin Nairobin kasar Kenya shugaban Najeriya Buhari ya kira kasashen Afirka da su gaggauta cudanyar cinikayya tsakaninsu da zummar samun tattalin arziki baidai

Yayinda yake jawabi a wata liyafar karramashi a karshen ziyarsa zuwa kasar Kenya, shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace fadada harkokin kasuwanci tsakanin Kenya da Najeriya cikin 'yan shekaru da suka gabata kamata ya yi a samu irin hakan a duk cikin kasashen Afirka.

Shjugaban yace fadada kasuwanci tsakanin kasashen Afirka shi zai sa a samu habakar tattalin arziki a nahiyar. Ya cigaba da cewa yanzu "Muna da 'yan kasuwa daga Najeriya suna kafa ma'aikatar sarafa siminti a Kenya yayinda kamfanonin sadarwa a Najeriya ke bin sawun harkokin bankunan tafi da gidanka da Kenya ke yi saboda wata hanya ce ta habbaka harkokin kudi musamman a yankunan karkarar Najeriya"

Shugaba Buhari yace "Muna da manoma daga Najeriya dake zuwa Kenya su koyi yadda manoman kasar suke samun nasara. Haka ma wasu 'yan kasuwan Kenya dake harakar man fetur da iskar gas suna hada hannu da kamfanonin mai na Najeriya"

Muna da 'yan Najeriya dake shan kofin Kenya a gidajensu da ofisoshinsu yayinda akwai 'yan Kenya da yawa suna sauraron wakokin Najeriya da kuma kallon finafinan Nollywood din Najeriya".

Irin wadan nan harkokin sun nuna cudanya a nahiyarmu kuma sun wuce cudanyar diflomasiya kawai. Idan aka samu cudanya haka a duk fadin Afirka babu shakka za'a kirkiro miliyoyin ayyuka a nahiyar ma 'yan Afirka, inji shugaba Buhari.

Shugaban yana fata Najeriya da Kenya zasu cigaba da gina cudanyar cinkayya dake da anfani ga kasashen biyu tare da kaiga gina tattalin arziki tsakaninsu.

Shugaban ya kira a hanzarta yin anfani da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka riga suka cimma da kuma kafa kwamitin hadin kai kan harkokin tattalin arziki.

Shugaban yace "yadda gwamnatocinmu biyu ke kara yin cudanya tare zai sa su ma 'yan kasuwar kasashenmu su kara kaimi wajen yin kasuwanci tare da fadada harkokin tattalin arziki".

Shugaban yace a karshen wannan ziyara ina da karfin gwuiwa cewa za'a kafa hanya kwakwara dangane da mutanen kasashen biyu da zasu dinga yin balaguro da da dakon kaya da saye da sayarwa .

Daga karshe shugaban Kenya, mai masaukin bako, Uhuru Kenyatta ya sanar cewa shugabannin biyu sun amince su karfafa dankon zumunci a harkokin kasuwanci da saka jari da yaki da cin hanci da rashawa da ta'adanci

XS
SM
MD
LG