Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Nada Muazu Sambo A Matsayin Karamin Ministan Ayyuka Da Gidaje


Shugaba Buhari, dama, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, hagu

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon karamin ministan ayyuka da gidaje, Muazu Jaji Sambo, a fadar gwamnatin kasar dake birnin tarayya Abuja, jim kadan gabanin bude taron kwamitin tsaro na kasa da aka gudanar a yau juma’a

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya fitar a shafinsa na Facebook.

A farkon wannan makon, majalisar tarayya ta amince da naɗin Mua'zu Jaji Sambo a matsayin sabon ministan, bayan shugaba Buhari ya aike musu da sunan shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa nadin ya biyo bayan maye gurbin tsohon ministan wutan lantarki Mamman Sale daga jihar Taraba da aka so a ba shi, sai kuma aka bashi matsayin karamin ministan ayyuka da gidaje

Wadanda suka samu halartar taron na tsaro sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ministan harkokin ‘yan sanda da na shari’a datsaro da kuma harkokin cikin gida da na kasashen waje. Da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro.

XS
SM
MD
LG