Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Sake Jaddada Aniyarsa Na Fadada Tattalin Arzikin Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Jiya Laraba a Abuja Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sake jaddada kudurinsa da na gwamnatinsa na ganin ya fadada tattalin arzikin kasar cikin dan karamin lokaci lokacin yake bankwana da jakadun kasashen Iran da China

Yayainda yake jawabi a wurin liyafar bankwana da aka shiryawa jakadan kasar Iran Saeed Koozechi, shugaba Buhari yace yayi imani cewa da dagewa tare da yin aiki tukuru da kishin kasa, Najeriya zata samu dogaro ga kanta ta samu ta sarafa duk abubuwan da yanzu take shigo dasu daga kasashen waje.

Shugaba Buhari yace "mun yi babban kuskure da muka dogara ga man fetur kawai domin samun kudin shiga muka kuma gina tattalin arzikinmu a kansa. Yanzu muna cikin halin kakanikayi saboda faduwar farashen mai a kasuwar duniya"

Ya cigaba da cewa "mun ga alfanun gina tattalin arziki akan abubuwa da dama ban da mai kamar yadda kasar Iran tayi lamarin da ya taimaketa rayuwa cikin shekarun da aka kakabamata takunkumi. Gashi yanzu tana tsaye daram duk da faduwar farashin mai"

"Yanzu kam mun dukufa kaindanain mu fadada tattalin arzikinmu zuwa wasu abubuwa. Yawancin kayan da muke sayowa daga waje muna iya sarafasu mu rage kashe kudi. Saboda haka mun kuduri aniyar cimma sarafa kayan da muke anfani dasu ba sai mun sayosu daga waje ba", inji Shugaba Buhari a cikin jawabinsa ga jakadan Iran.

A wani halin kuma yayinda ya karbi jakadan kasar China Mr. Gu Xiaojie wanda ya zo ya yiwa shugaban bankwana saboda ya kammala wa'adinsa a Najeriya Shugaba Buhari ya bashi tabbaci cewa Najeriya zata cika nata alkawarin bisa yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi domin inganta wasu ma'aikatu da gina tsarin da ake bukata da suke da mahimmanci domin gina tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban yace sabili da mahimmancinsu ga kasar gwamnatinsa zata mutunta yarjeniyoyin da kamfanonin China domin sake gina ma'aikatu da masana'antun da ta gada daga gwamnatin da ta shude ta kuma tabbatar duk ayyukan an kammalasu.

Shugaba Buhari ya sake jaddada aniyarsa cewa lallai sai an kammala gina tashar makamash da aka soma ginawa a Mambila. Tashar tana da mahimmanci ga kokarin gwamnati na ganin kasar ta rage dogaro ga iskar gas domin samun wutar lantarki.

Shugaba Buhari ya yabawa jakadun dangane da kokarinsu na karfafa dangantaka tsakanin kasashensu da Najeriya yayinda suke Abuja.

Yayi masu fatan alheri bisa duk abubuwan da suka sa gaba a koina suke.

XS
SM
MD
LG