Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Sauka Lafiya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja babban birnin kasar bayan doguwar jinya a London inda yayi jinyar wata cuta da ba a bayyana ba.

Shugaba Buhari dai ya bar Najeriya tun ranar bakwai ga watan Mayu, kuma tuni wadansu yan Najeriya suka fara kira da ya koma bakin aiki ko kuma ya sauka daga karagar mulki.

Magoya bayansa sun yi layi bisa tituna kan hanyar tashar jirgin sama, yayin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibajo, wanda yake rikon mukamin shugaban kasa yaje tarbar Buhari a tashar jirgin sama.

Shugaba Buhari ya fara tafiya jinya birtaniya ne a watan Janairu, inda ya zauna na kusan watanni biyu kafin ya koma gida a watan Maris, ya kuma sake tafiya jinya a watan Mayu.

A lokacin da yake jinya, shugaba Buhari yaba mataimakinsa Yemi Osinbajo ikon gudanarda harkokin mulki.

A farkon makon nan masu zanga zanga suka gudanar da gangami a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya dauke da kwalaye dake cewa, “Ka dawo ko kuwa kayi murabus” an kuma gudanar da irin wannan gangamin a birnin Ikko.

Ranar talata, magoya bayan Buhari suka yi fito na fito da wadansu masu zanga zangar a wata kasuwa dake Abuja, bisa ga rahotannin kafofin sadarwar Najeriya.

Sanarwar da aka bayar ta dawowar Buhari ta kuma ce, shugaban kasar zaiyi jawabi ga kasa ranar Litinin da safe.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG