Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Fara Ziyarar Aiki Anan Amurka Lahadin Nan


Shugaba Buhari a Abuja bayan sallar Eid.

Ranar lahadin nan ne ake sa ran shugaban na Najeriya zai fara ziyarar aiki na kwanaki hudu

Idan Allah Ya kaimu Lahadi ne ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara rangadin kwanaki hudu anan Washington DC, inda zai gana da shugaban Amurka Barack Obama.

Ana jin barazanar da Boko Haram take yi a kasar zai kasance jigo a shawarwarin da shugabannin biyu zasu gudanar a fadar White House ta shugaban Amurka ranar litinin. Amurka tana son ta fadada irin gudumwar da take baiwa Najeirya wajen yaki da 'yan binidgar, wadanda suka zafafa kai hare hare da suke yi tun bayan da shugaba Buhari ya kama aiki cikin watan Mayu.

Haka nan ana kyautata zaton shugabannin biyu zasu tattaunawa kan kudurin sauye sauyen siyasa da na tattalin arziki da nufin kawo karshen cin hanci da rashawa da kusan ya zama gama gari a kasar.

Wannan shine karon farko da shugaba Buhari zai kawo ziyara anan Amurka tun bayan da ya sami nasara a zaben shugaban kasar da aka yi cikin watan Maris, da kuma mika mulki cikin tsanaki abunda ba'a saba da ganinsa a Najeriya.
Duka kasashen biyu suna nuna dokin inganta dangantaka bayan tsamin da aka shiga na shekaru zamanin mulkin shugasba Jonathan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG