Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Canza Dalilin Da Ya Bayar Na Korar Michael Flynn


U.S. -- Gen. Michael Flynn, former national security adviser to US President Donald Trump, arrives at Federal Court in Washington, December 1, 2017

Ana iya cewa an samu rudani ko kuma bayanai masu karo da juna daga kalaman shugaba Donald Trump na dalilin da yasa ya kori tsohon mai bashi shawara a harkokin tsaro

Yanzu ana iya cewa shugaban Amurka ya sauya matsayin sa jiya asabar game da dalilin da yasa ya kori tsohon mai bashi shawara a harkan tsaro Michael Flynn.

Da farkon shugaban yace dalilin da yasa ya kore shine domin bai fada wa mataimakin shugaban kasa Micheal Pence gaskiya ba game da huldar sa da Rasha lokacin da ake shirye-shiryen mika mulki ba.

Amma kuma kwaran sai gashi a shafin sa na tweeter shugaba Trump ya rubutta cewa dalilin dayasa ya kori Flyn shine domin ya shirga wa mataimakin shugaban kasa karya shida hukumar binciken manyan laifuka ta FBI,Kuma ya amsa wadannan laifuffuka,

Shugaba Trump yace wannan abin kunya ne, yace abinda Flyn yayi a lokaci shirye-shiryen mika mulki ba abu ne da ya sabawa doka ba, kuma ba wani abin boyo a cikin sa.

A cikin wannan sakon na shafin tweeter na shugaban kasa ya nuna a zahiri cewa shugaba Trump na sane da cewa Flynn ya shara wa FBI karya ne da kuma mataimakin shugaban kasa, harma da dangantakarsa da kasar Rasha, Sai dai Shugaba Trump bai bayyana FBI ba da farko game da Flyn da kuma abinda ke tsakanin sa da Rasha ba.

Dokar Amurka ta hana yiwa hukumar FBI karya.

Har wayau dai a cikin shafin na shugaba Trump a tweeter na yau lahadi yace sam shi bai umurci tsohon shugaban hukumar ta FBI James Comey ya dakatar da binciken Flynn ba wannan ma wani labarin karya ne gamasu yayata shi game batun Comey.

Yanzu dai wannan sakon na shafin Tweeter na shugaba Trump ba abinda ya haifar sai rudani akan abin da ya sani game da huldan Flyn da Rasha

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG