Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Zai Rattaba Hannu A Sabuwar Dokar Bakin Haure


Donald Trump

Kafafen yada labarai a nan Amurka sun rawaito cewa Shugaban Kasar Amurka Donald Trump na tsammanin sake rattaba hannu akan wata sabuwar doka ta musamman a gobe Litinin wacce ta shafi Bakin haure da kuma tafiye tafiye zuwa Amurka , bayan Kotun gwamnatin tarayya ta dakatar da yunkurin gwamnatin na baya.

Ba’a sami cikakken bayanin sabuwar dokar ba har ya zuwa daren jiya asabar, amma duk da haka Kamfanin dillancin labarai na Associate Press ya bada rahoton sabuwar dokar hana tafiyar bazata hada da Iraqi ba a cikin jerin sunayen kasashe bakwai masu yawan musulmi da dokar ta ke akansu kamar yadda aka auna.

Kotun gwamnatin tarayya ta dakatar da haramcin tafiyar na ranar 27 ga watan Janairu wacce ta haramtawa yan kasashe guda bakwai masu yawan musumai shigowa Amurka na wucin gadi, wadanda suka hada da Iraqi da Iran da Libya da Somaliya da Sudan da Siriya da Kuma Yemen, dokar ku ma ta tsaida shirin yan gudun hijirar Amurka.

Trump dai ya bayyana damuwarsa ne dangane da ‘Yan ta’adda a yayin da yayi saurin saka hannu akan hana shigowa Amurka na wucin gadi.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG