Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalan Shugaban Tsagerun Naija-Delta Sun Tabbatar Cewa An Kashe Shi


IYalan shugaban mayakan sa kan Naija-Delta sun ce an masa kofar rago ne aka kashe shi.

Iyalan wani shugaban mayakan sa kan Naija-Delta wanda ake zargin sa da hannu a magudin zabin 2007, sun ce an kashe shi ne bayan an masa kwantan bauna, koda yake har yanzu ba su ga gawarsa ba.

Shi dai Soboma George, shugaban haramtacciyar kungiya mai ban tsoro, ya bace ne tun bayan harbin da ya auku a birnin Fatakwal ran Talata.

‘Yan sanda sun fadi yau Alhamis cewa wani danginsa mai suna Chief Adiele George ya gaya masu cewa iyalansa sun sami bayanin cewa an kashe shi. To saidai babu wanda ya gan shi ko ya bayyana gawarsa.

‘Yan sanda sun ce au magoya bayan Soboma George ne su ka boye gawarsa au maharan ne su ka boye gawar.

Harbin ya faru ne daura da wani filin kwallon kafa a daidai lokacin da George din ke barin wurin da tawagarsa. An kuma kashe wata mata aka ji wa wata kuma rauni a wannan harbin.

XS
SM
MD
LG