Accessibility links

ZABEN2015: Shugaba Jonathan Ya Ziyarci Adamawa Karo Na Uku

  • Grace Alheri Abdu

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kai ziyara karo na uku cikin wata guda a jihar Adamawa, a wannan karon da nufin dinke barakar dake tsakanin ‘ya’yan jam’iyarsa ta PDP.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kai ziyara karo na uku cikin wata guda a jihar Adamawa.

A wannan karon, shugaba Jonathan ya je jihar ne da nufin dinke barakar dake tsakanin ‘ya’yan jam’iyarsa ta PDP dake neman maida hannun agogo baya a yunkurin jam'iyar na ci gaba da rike madafun iko a jihar.

Wannan ya biyo ci gaba da sa in sa da ake yi tsakanin 'ya'yan jam'iyar ana kasa da makonni biyu da gudanar da babban zabe na kasa. Wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz na dauke da ci gaban rahoton.

XS
SM
MD
LG