Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Idriss Deby Ya Lashe Zaben Kasar Chadi


 Shugaban kasar Chadi Idriss Deby
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby

Shugaban kasar Chadi Idris Deby ya lashe sabon wa’adi wanda wannan shine karo na biyar, a kan karagar mulki. Deby ya buge abokan karawar sa har su 13 da gagarumar tazara, sai dai ‘yan adawar sun zarge shi da tafka magudi a zaben.

A cikin sanarwar da hukumar zaben kasar ta bayar ta ce Shugaba Deby, ya lashe zaben da kashi 61 da rabi cikin 100 na dukkan kuri’un da aka jefa, inda ya ba babban madugun ‘yan adawa , Sale Kebzado, ratar kusan kashi 50. Sai dai Kebzado yace ba komi cikin zaben sai magudi.

Kebzado shi da sauran ‘yan takarar sunce basu yarda da sakamakon wannan zaben da suka bayyana a zaman na “fashin kuri’u” ba suna zargin shugaba Deby da jibge katin zabe kafin a jefa kuria.

Suka ce daruruwan akwatunan zabe sunyi layar zana kana Shugaba Deby ya kulle sojoji masu yawa da suka yi niyyar kin jefa masa kuria.

Sai dai kuma a waje daya masu sa ido daga Tarayyar Kasashen Afirka sun bayyana cewa an gudanar da zaben ba tare da magudi ba.

Ita ko hukumar zaben kasar tace mutane sama da miliyan 6 ne suka jefa kuri’ar kuma an samu a kalla kashi 75 da suka fito, kuma tunda Deby ya samu sama da kashi 50, Kenan ba bukatar zabe zagaye na biyu.

XS
SM
MD
LG