Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jacob Zuma Na Afirka Ta Kudu Yayi Murabus Nan Take


Jacob Zuma
Jacob Zuma

Jacob Zuma yayi jawabi ga al'ummar kasar inda yace ba ya tsoron kuri'ar rashin amincewa da gwamnatinsa a majalisar dokoki, amma sai ya juya yace yayi murabus nan take

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, wanda aka hana ma jin sakat, yayi murabus nan take a jiya laraba da maraice.

Zuma, mai shekaru 75 da haihuwa, ya amsa umurnin jam'iyyar ANC mai mulki, wadda ta matsa masa lamba a kan yayi murabus ya kawo karshen mulkin shekaru 9 da yayi cikin yanayi na abubuwan ban fallasa.

A coikin jawabin minti 30 da yayi ga kasar, Zuma yace rashin adalci ne ga jam'iyyar ANC ta bukace shi da yayi murabus.

Duk da ikirarinsa na cewa jam'iyyar ANC ba ta bi ka'ida wajen neman yayi murabus ba, Mr. Zuma yace, "Na yanke shawarar yin murabus daga kujerar shugabancin kasa nan take. Duk da cewa ban amince ad shawarar shugabannin jam'iyya ta ba, na kasance dan jam'iyyar ANC mai bin umurni."

Zuma ya kara da cewa, "A yayin da nake barin wannan kujera, zan ci gaba da aiki ma al'ummar Afirka ta Kudu, da kuma ANC, kungiyar da na yi ma aiki duk tsawon rayuwata."

Ana sa ran majalisar dokokin Afirka ta Kudu zata zabi shugaban ANC, Cyril Ramaphosa, a matsayin shugaban kasa a yau alhamis ko gobe Jumma'a.

A wannan makon shugabannin jam'iyyar ANC suka yanke shawarar neman Zuma yayi murabus bayan da ya shafe shekaru 9 yana mulki, inda aka fuskanci tabarbarewar tattalin arziki da kuma zarge-zargen zarmiya da cin hanci.

Zarge-zargen da ake masa sun hada har da cewar ya kyale iyalan Gupta masu arziki suna sanya baki kan mutanen da zai nada ministocinsa, da kuma zargin cewa yayi amfani da kudi dala miliyan 20 na gwamnati wajen gyara gidansa na kashin kansa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG