Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan bai yi Wata Rawar Gani ba


Shugaba Goodluck Jonathan.

Shugaba Goodluck Jonathan na daya daga cikin shugabanan da suka dade suna mulki a kasar Najeriya amma wasu sun koka da mulkin shugaban, akan cewa ba a sami wani cigaba ba.

A karshen makon da ya gabata, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fito yace, shugaba Jonathan bai yi wata rawar gani ba a Tsawon shekarun da yayi yana mulki.

A wata hira da muryar Amurka tayi da Dr. Abubakar Sadiq mai fashin baki akan harkokin siyayasa, ya fadi cewa wannan zancen gaskiyane don babu fannin da aka sami cigaba a Najeriya.

Dr. Sadiq yaci gaba da bayani akan irin rashin cigaban da aka samu a kasar musamman a fannonin wutar lantarki, tsaro da tattalin arziki da sauransu, sai ma dai tarin bashi da aka ci ba kuma abin azo a gani. Ya kuma kara da cewa duk da cewa abinda tsohon shugaba Obasanjo ya fadi gaskiya ne, yana (Obasanjo) da hannu a halin da Najeriya ke ciki yanzu, don shine ya sa shugaba Jonathan kan kujerar mulki a ta bakin Dr. Sadiq.

Daga karshe Dr. Sadiq yayi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi shugaba mai hangen nesa, mai adalchi, wanda zai sa muradan ‘yan Najeriya gaban nashi a zabe mai zuwa.

ga cikakkiyar hirara da Bello Habeeb Galadanchi ya yi da Dr. Abubakar Sadiq.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

XS
SM
MD
LG