Korea ta Arewa, ta sake harba wani makami mai linzami kirar Ballistic, matakin da ya saba alkawarin da ta yi wa Shugaba Donald Trump na cewa ba za ta sake gwajin makamin ba.
Korea ta Arewan ta yi alkawarin dakatar da duk gwaje-gwajenta idan Amurkan da Korea ta Kudu suka kammala atisayen hadin gwiwa da suka yi.
Ko da yake, Shugaba Trump ya ce, shi ba ya kallon wannan gwaji a matsayin karya alkawari.
Ya bayyana hakan ne gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa taron kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya na G 7.
Wani babban jami'i a gwamnatin Korea ta Kudu, ya ce har yanzu, suna fatan akwai kofar tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California