Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Kim Jong Un Na Koriya Ta Arewa Ya Bayyana


Shugaba Kim Jong Un

Bayan da rahotannin kafafen labarai da dama su ka yi ta cewa Shugaban Koriya Ta Arewa na fama da matukar rashin lafiya idan ma bai mutu ba, sai gashi Kim Jong Un ya sake bayyana cikin jama’a, a karo na farko ciki kwanaki 21, a wani kamfanin yin takin zamani.

Gidan radiyon gwamnatin Koriya Ta Arewa ya ce jiya Jumma’a Shugaba Kim ya halarci bukin kammala kamfanin takin zamni danke Sunchon, birni mai tazarar kilomita 50 arewa da Pyongyang, babban birnin kasar.

Nan take dai kafar labaran ta gwamnati ba ta wallafa wani bayani mai dauke hoto ko bidiyon Kim a wurin ba, wanda aka ce ya je tare da kanwarsa, Kim Yo Jong, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Jita jita game da halin da Kim ke ciki ta fara bazuwa ne bayan da ya kasa halartar bukin zagayowar wani muhimmin al’amari na siyasar kasar a ranar 15 ga watan Afirilu. Rabon a ganshi a bainar jama’a tun ranar 11 ga watan Afirilu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG